✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Man da Najeriya take hakowa bai wuce ganga 1.3m ba a kullum’

Gwamnan ya ce akwai yiwuwar adadin ya karu zuwa ganga miliyan 1.5 kafin Buhari ya sauka daga mulki ya mika wa Tinubu.

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce Najeriya na hako danyen mai ganga miliyan 1.2 zuwa miliyan 1.3 kowace rana, sabanin ganga kusan miliyan biyu da aka ware mata.

Sai dai ya ce akwai yiwuwar adadin ya karu zuwa ganga miliyan 1.5 kafin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulkin kasar ya mika wa dan takararsu na APC, Bola Tinubu.

A hannu guda kuma, Gwamnan ya ce dan takarar nasu na Shugaban Kasa zai mulki Najeriya na wa’adin shekara takwas.

Kazalika, ya ce ko kusa, Tinubu ba abin kwatantawa ba ne da dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi.

Sule ya ba da misalin yadda tattalin arzikin Jihar Legas ya habaka fiye da na Anambra, jihar da Peter Obi ya mulka tsawon shekara takwas.

Gwamnan ya ce fannin man fetur na Najeriya zai bunkasa kafin karewar wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.