✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mamman Daura: Ba na zakewa a wurin Buhari

Mamman Daura ya amayar da abin da ke cikinsa kan zargin juya Buhari

Malam Mamman Daura, wanda aka ganin ya fi kowa kusanci da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce bai taba zakewa ba wajen ba wa Buhari shawara ba.

Wannan shi ne karon farko da Mamman Daura ya yi aman abun da ke cikinsa kan zarge-zargen da ake yi masa cewa yana cikin masu juya akalar mulkin Shugaba Buhari.

Daura ya taso tare da Buhari, a tattaunawar da BBC Hausa ta yi da shi ya ce: “Eh, ina zuwa kuma in ya tambaya ina ba shi, amma ba zan je ba da kaina in zake in ce na zo in ba shi shawara, ko zan yi kaza, zan yi kaza. A’a, ba a yin haka ga gwamnati”.

Ya fadi hakan ne bayan an tambaye shi alakarsa da Shugaba Buhari da kuma ko yankan ziyarce shi ko ya ba shi shawara.

Dangane da zaben 2023, Mamman Daura ya ce “Karba-karba an yi sau daya, an yi sau biyu an yi sau uku. Ya kamata kasar nan mu zama wanda ya fi dacewa ya cancanta ba wanda ya fito daga wuri kaza ba”.

Ra’ayin nasa ya yi daidai da na marigayi Samaila Isa Funtua, a lokacin da aka yi masa kwatankwacin wannan tambaya a gidan talbijin.

Ta fannin dangantakarsu da Buhari, Mamman Daura ya ce Buhari “Kanen babana ne. Babana shi ne na farko da mahaifiyarsu ta haifa, Janar Buhari shi ne na karshe”.