Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta ce wasu daga cikin mambobinta sun fara sayar da gidajen mansu saboda rashin ciniki tun bayan cire tallafin mai.
Shugaban kungiyar na kasa, Chinedu Okoronkwo, ne ya bayyana haka a yayin wani taron jin ra’ayin jama’a a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken karin farashin man fetur da aka yi a kwanan baya a ranar Talata.
- Ba zai yiwu gwamnati ci gaba da bayar da tallafi a bangaren lantarki ba – El-Rufa’i
- KAI-TSAYE: Yadda Majalisa ke tantance Ministocin Tinubu
A cewarsa, a garin Ibadan na jihar Oyo, sama da mambobi 40 ne suka rufe gidajen mansu a kasuwa.
Ya kara da cewa, mambobin kungiyar da yawa na shirin sanya gidajen mansu a kasuwa sakamakon karancin kasuwanci da suke samu.
Ya ce da yawa daga cikin mambobin da ke sayar da babbar mota na man fetur cikin kwanaki uku yanzu na daukarsu wata guda kafin su sayar.
Okoronkwo ya ce duk mota ana sayar da ita kimanin Naira miliyan 25, wanda dilallan ba sa samun ribar Naira 500,000.
Ya ce ribar da ake samu ba ta isa a biya albashin ma’aikata da kuma biyan wasu bukatu da suka shafi haraji.
Shugaban na IPMAN, ya koka da yadda asusun samar da albarkatun man fetur (PEF) da kuma kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ke rike da naira biliyan 750 na kudaden da ake bin mambobin kungiyar.
A cewarsa, yayin da PEF ke rike da naira biliyan 250, ita kuma NNPCPL na rike da naira biliyan 500.
Sai dai IPMAN ta shawarci gwamnati da ta kafa tsare-tsare don karfafa amfani da iskar Gas (CNG) a madadin man fetur.
A cewarsa, ya kamata Najeriya ta yi amfani da dimbin iskar gas da ake da shi duk shekara a matsayin wata hanyar da za a samar da makamashin ababen hawa.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kwamitin wucin gadi, Babajimi Benson, ya ce an kafa kwamitin wucin gadi ne domin ya binciki halin da ake ciki na karin farashin man fetur daga N537 zuwa N617.
“Babu shakka man fetur shi ne jigon tattalin arzikin Najeriya kuma duk wani karin farashinsa babu shakka zai haifar da tashin farashin kaya da ayyuka musamman kayan abinci.
“Kididdiga ta nuna cewa ‘yan Najeriya na kashe kusan kashi 80% na abin da suke samu a abinci kadai. Wannan ne ya sa muke fargabar cewa wannan karin da aka yi a baya-bayan nan na iya jefa ‘yan Najeriya cikin talauci.
“Wannan kwamitin na da yakinin cewa gwamnati tana daukar matakin da ya dace. Wannan shi ne abin da muke son ji a wannan binciken. Ya kamata ‘yan Najeriya su fahimci dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki,” in ji shi.