Wata daliba ’yar aji biyar a matakin sakandare, Hauwa’u Salihu, ta samu lahani a kashin bayanta sakamakon dukan wuce misali da malaminta na darasin lissafi ya lakada mata a Zariya, Jihar Kaduna.
Mahaifin Hauwa’u ya ce kawo yanzu ya kashe kudi sama da Naira miliyan daya kan jinyar ’yar tasa kuma har yau yana kan kashewa tun da jinyar ba ta kare ba.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a kauyen Kaduna
- Ranar Alhamis masu gidajen burodin Najeriya za su fara yajin aiki
Ana zargin malamin, mai suna da ke koyarwa a Makarantar Gidauniyar Rochas da ke Zariya ya yi amfani da wani katon sanda ne wajen zane dalibar mai suna Hauwa’u Salihu tare da wata kawarta a lokacin da ake tsaka da darasinsa saboda sun yi masa azarbabi.
Da take labarta wa Aminiya yadda lamarin ya auku, Hauwa’u ta ce: “Lokacin da malaminmu na lissafi, Malam Isah ya shigo ajinmu, sai ya yi rubutu a allo ya ce mu kwafe idan cikin litattafanmu idan ya kammala bayani.
“Amma sai ni da kawata muka soma kwashe rubutun, a lokaci da shi kuma yana kan bayani, kwatsam sai ya gano mu.
“Daga nan ya dauki wani katon sanda wanda masu gadi suka ajiye a ajin ya doke mu da shi.
“Kawata ta yi kokarin kare dukan da hannunta wanda hakan ya yi sanadiyar yi mata rauni a hannu.
“Yayin da ni kuma na yi kokarin kauce wa dukan, a nan ne sandan ya same ni a baya.
“Bayan da na dawo gida ne na ji zafin wurin sosai wanda hakan ya sa mahaifiyata ta dauke ni zuwa asibiti mafi kusa don yi mini magani.
“Bayan kwanaki, sai na ji ciwon na karuwa wanda hakan ya shafi kafafuna da kuma hannu da har ya kai ga ina wahala wajen motsa su.
“Daga nan ne aka dauke ni zuwa Asibitin Koyarwa na ABU da ke Zariya, inda a nan aka tabbatar na samu matsala a wuyana wanda ya kusa da yi wa kashin bayana lahani.”
Wakilinmu da ya ziyarci gidan su daliban mai suna Hauwa’u da ke Tudun Jukun, Zariya, inda ya gana da mahaifinta Malam Salihu Umar da aka fi sani da Dan Ali.
Malam Salihu ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu Hauwa’u na ci gaba da jinya bayan sallamo ta da aka yi daga Asibitin Koyarwa na ABU da ke Shika a Zariya, inda aka yi mata wasu jerin gwaje-gwaje.