Sarkin garin Fatika, da ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Umar Farouk, ya nada malamin jami’a kuma marubucn littattafai Dokta Audi Tanimu Giwa a matsayin Shettiman Fatika a fadarsa a makon jiya.
An haifi Dokta Audi ne a garin Giwa a 1961, kuma ya halarci makarantar firamare ta LEA Kofar Kuyambana daga 1970 zuwa 1975, sannan ya halarci Kwalejin Gwamnati ta Kaduna daga 1975 zuwa 1980, inda ya zarce Kwalejin Ilimi Mai zurfi da ke Zariya daga 1980 zuwa 1983.
A 1983 zuwa 1986 ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya yi digiri a harshen Ingilishi, sannan ya yi digiri na biyu da digirin digirgir duk a harshen Ingilishi.
Sabon Shettiman, shi ne Shettima na 20 a wannan tsohuwar masarauta. Kuma ana bada wannan sarauta ce ga wanda yake da ilimi da gaskiya da tawali’u, kuma aikinsa shi ne ya bada shawara game da yadda za a ciyar da kasa gaba. Sabon Shettiman Fatika, Dokta ne na harshen Ingilishi a Jami’ar Jihar Kaduna.
Dokta Audi ya kafa tarihi inda ya fi dadewa a kan kujerar mai kula da dalibai don ya kwashe shekara goma sha daya.
Sannan ya taba rike mukamin Shugaban Sashin Harshen Ingilishi na Jami’ar Jihar Kaduna. Ya fara koyarwa ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Masarautar Fatika da ta takwarorinta na Kauru da Kajuru da Dumu (Makarfi) tarihi ya nuna sun riga Masarautar Zazzau kafuwa.