✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Malami ya kashe abokinsa da shinkafar bera

Ya ja abokin nasa zuwa wani kangon gini ne inda ya zuba masa shinkafar bera a cikin damammiyar fura da nono.

Ana zargin wani matashin malamin makaranta a Jihar Katsina da kashe abokinsa ta hanyar amfani da maganin bera.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyana cewa, suna tsare da malamin kuma sun gano ya kashe abokin nasa ne bayan da ya ja shi zuwa wani kangon gini da ke yankin Mani.

“Wanda ake zargin ya ja abokin nasa zuwa wani kangon gini inda ya ba shi fura da nono da ya zuba guba a ciki.

“Bayan da ya sha furar sai ya fita hanyacinsa, ya kasa gane inda yake.

“Daga nan ya dauki itace ya maka masa a kai har ya kashe shi, sannan ya dauki gawar ya jefa a wata rijiya da ke gidan,” in ji shi.

SP Gambo ya ce bayan haka ne wanda ake zargin ya sace motar marigayin ya kara gaba da ita.

Ya kara da cewa, marigayin jami’i ne a hukumar tsaro ta NSCDC, wanda kuma yake ajin karshe a Kwalelin Ilimi ta Ta Tarayya (FCE) da ke Katsina.

A cewarsa, binciken ’yan sanda ya gano cewa daga bisani, wanda ake zargin ya kira matar marigayin a waya kan abin da ya shafi takardun motar mijinta.

Isah ya ce sakamakon binciken da suka gudanar, sun gano motar mamacin da kuma maganin bera da itacen da ya yi amfani da shi wajen kisan a wajen wanda ake zargin, kuma ya amsa laifin.

Ya ce za gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

(NAN)