Ɗan Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya musanta zargin kisan wani mutum a ƙasar Indiya.
A bayan nan dai wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa, ɗan gwamnan na Jihar Borno mai suna Umara Zulum Umara, ya kashe wani mutum a ƙasar Indiya.
Masu yaɗa jita-jitar sun yi zargin cewa Umara Zulum wanda ɗalibi ne a wata jami’a da ke birnin New Delhi na ƙasar Indiya, ya kashe wani mutumin ƙasar Sin ta hanyar rotsa masa kwalbar barasa a kansa saboda ya kula wata budurwa wadda shi ma ya ƙyalla ido a kanta a wani gidan rawa.
Tuni dai gwamnatin Borno ta yi watsi da wannan jita-jitar da ta ce har an kama ɗan gwamnan kan zargin kisan kai.
Da yake musanta rahoton cikin wata sanarwa a ranar Laraba, mai magana da yawun Gwamnan Borno, Abdurrahman Ahmed Bundi, ya ce babu ko ɗaya daga cikin ’ya’yan gwamnan da aka kama ko ake tuhuma da wani laifi ko saba wa wata doka a ko’ina.
Hadimin gwamnan ya buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan sannan kuma su tanadi rariyar tace duk wani rahoto domin tabbatar da sahihancinsa kafin su yaɗa shi.
Shi ma ɗan gwamnan wanda jita-jitar ta shafa, ya magantu a wannan Alhamis ɗin, inda ya bayyana lamarin a matsayin marar tushe ballantana makama.
Cikin wani hoton bidiyo mai tsawon daƙiƙa 35 da ya wallafa a dandalin sada zumunta, Umara ya ce masu yaɗa jita-jitar ba su da wata manufa face ɓata sunan mahaifinsa.
A cikin bidiyon da rahotanni ke cewa an naɗe shi a Fadar Gwamnatin Borno da ke birnin Maiduguri, Umara ya ce “ya ku ’yan Nijeriya. Ni ne Umara Babagana Umara Zulum. Ina so na yi ƙarin haske kan shacin-faɗin da aka yi a kaina.
“Na samu labarin cewa ana yaɗa wata gulma da ba ta da asali wadda ake zargin na kashe wani a gidan rawa.
“Wannan ba gaskiya ba ne. Manufar waɗanda suka ƙirƙiro labarin ita ce ɓata sunan mahaifina.
“Ina nan zaune a gida tare da dangina kusan watanni biyu ke nan yanzu a cikin Maiduguri.”