Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewa kimanin malamai dubu 21 da 780 daga cikin malamai dubu 33 suka fadi a jarabawar aji hudu na firamaren da aka shirya musu don a gwada kwarewarsu.
El-Rufa’i wanda ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin tawagar Bankin Duniya ya ce jihar tana son daukar malamai kimanin dubu 25 a shirinta na dawo da martabar ilimi a jihar.
“Mun gwada malamai dubu 33 na makarantun firamare ta hanyar basu jarabawar ’yan aji hudu na firamare. An sa ran za su ci kashi 75 cikin dari amma abin haushi sai aka bayyana cewa kashi 66 cikin dari na malaman ba su sami kason da ake bukata ba. An siyasantar da yadda ake daukar malaman makaranta a baya amma a yanzu muna son daukar malamai matasa da suka kware don su tallafa wa ilimi a jihar”. Inji shi.