Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta bankado kimanin malaman makaranta 3,268 da take biyan albashi domin su koyar a makarantun gwamnati amma suka bige da koyarwa a makarantun kudi.
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakinta, Aliyu Yusuf ya fitar a Kano ranar Talata.
Matakin dai na zuwa ne kasa da makonni uku bayan Gwamnatin Jihar ta umarci a mayar da kimanin ma’aikatan Jihar 5,000 da ke da takardun shaidar koyarwa zuwa azuzuwa domin su ci gaba da koyarwa, a kokarin magance matsalar karancin malamai a Jihar.
Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne kwanaki uku da kafa wani kwamitin tantancewa da gwamnatin Jihar ta kafa domin yi wa malaman kiranye.
“Kwamitin, wanda ke karkashin Shugabancin Dokta Ibrahim Bichi ya gano cewa wasu malaman sun shafe sama da shekara 10 zuwa 15 suna koyarwa a makarantun masu zaman kansu, yayin da suke ci gaba da karbar albashi daga gwamnati, wasu kuma sun tafi karo karatu har zuwa matakin digiri na biyu da digirin digir-gir,” inji sanarwar.
Kazalika, kwamitin ya kuma gano yadda irin wadanna malaman ke ci gaba da samun karin girma har zuwa matakin Daraktoci.
Sanarwar ta kuma ce an gano wata makarantar kudi guda daya da take da irin wadannan malaman har guda 50 kuma ake biyansu daga lalitar gwamnati.
Gwamnatin ta bayyana hakan a matsayin wani koma-baya da ya zama wajibi a kawo karshensa kafin a magance matsalar karancin malamai a makarantun gwamnati.