Malama Halima Sa’idu fitacciyar mai da’awa ce. Ta zaga kauyuka don fadakar da mata, ta gina makarantun islamiyya, ba ta da wani buri face Allah Ya karbi ranta wurin yada addinin Musulunci. Ta bayyana dalilin da ya sa ta fara da’awah
Assalamu alaikum, sunana Hajiya Halima Sa’idu, an haife ni a Kaduna. Mahaifina shi ne Alhaji Sa’idu Mai Mota, daya daga cikin direbobin marigayi Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello. Na fara makarantar LEA a Unguwar Sarkin Musulmi a Kaduna, daga nan na fara makarantar sakandare ta kueens College; bayan mahaifina ya rasu sai aka dawo da ni makarantar ‘yan mata da ke Kawo ta Kaduna.
An yi mini aure da wuri amma ba a kai ni gidan mijina ba sai bayan da na kammala sakandare. Na yi makarantar Islamiyya ta Nurul-Islam, daga nan sai makarantar addini ta Salamatu Institute for Islamic Studies a Kaduna. Na fara aikin gwamnati a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a bangare masu binciken kudi. A shekarar 2006 na kammala karatun aikin malunta a Kwalejin Ilimi ta Zuba. Yanzu kuma ina koyarwa a sakandaren gwamnati da ke Dukpa a karamar Hukumar Gwagwalada, Abuja hade da gudanar da wa’azi.
Abin da ba zan manta da shi ba ina karama
Alhamdu lillahi, a lokacin da muke kanana a kullum burin mahaifinmu shi ne mu rika yin abubuwa masu kyawu. A wannan lokacin islamiyyar da muke zuwa tana kusa da gidanmu. Mukan yi karatun kur’ani da safe da kuma yamma, ba mu da lokacin wasa. Ina iya tunawa a lokacin mahaifinmu ne kawai yake da talabijin amma duk da haka ba mu da lokacin kallo, domin a kowane lokaci muna zuwa islamiyya, mukan samu lokacin hutu ne kawai Alhamis da Juma’a. Mahaifiyarmu ta saya mini karamar tukunya da nake koyon girki.
Yadda na fara wa’azi
Na fara karatun addini tun ina karama a wurin mahaifinmu duk da cewa shi ba malami ba ne. Mutum ne mai matukar son malamai, yakan yawaita kai musu ziyara. Duk lokaci da malamai suka zo unguwarmu yin wa’azi yakan ba su masauki. Wannan ya sanya na taso a cikin masana kuma dalilin da ya sa na fara karatun addini tun a gida ke nan.
A shekarar 1992 ni da tsohon mijina muka dawo gidajen Malaman Jami’ar Abuja da ke Giri, sai na fahimci babu masallaci ko islamiyya, hankalina ya yi matukar tashi daga nan na nemi mijina ya ba ni dama don na gana matan yankin, da haka al’amarin ya faro.
Na fara koyarwa tun a falon gidanmu da dalibai 11. Na fara koya musu karatun kur’ani da kuma wadansu littattafai, kafin a ce me tuni gidana ya cika. Daga nan ne wani mutum da ake kira Dokta Burra ya ba mu garejin gidansa muka ci gaba da karatu. Ana cikin haka aka kara yawa wurin ya sake yin kadan. Daga nan na fara tunanin yadda zan samu fili na gina makaranta, hakan ya sanya na je kauyen Giri na nemi ganin dagacin kauyen, a wannan lokacin ina da dubu 5 kacal. Bayan ya fahimci manufata sai ya ba ni filin kyauta. Daga nan na fara ginin da bulun kasa hade da taimakon wadansu ‘yan kauyen, da haka har muka gina aji daya, cikin ikon Allah sai mijin wata mata da ake kira Hajiya Rabi Wada Aliyu wanda mijinta tsohon Babban Sakatare ne a wata Ma’aikatar Tarayya a Abuja ya gina mana ajujuwa biyu. Wannan shi ne takaitaccen tarihin yadda na fara karantawa da wa’azi.
Ina son makaranta tun ina karama
Tun ina karama nake son makaranta. Ina son malamaina tun daga firamare har sakandare. Nakan kwaikwayi yadda suke rubutu bayan na dawo gida, wannan ne kuma ya dada ba ni sha’awar koyarwa.
Shakuwa tsakanin iyaye
Na fi shakuwa da mahaifina kuma ya fi mayar da hankali a kaina tun ina karama, zan iya tunawa ya so ya kai ni Libya a lokacin da yake da rai. Ya fara gudanar da wannan shirin ne shi da Sheikh Hassan Lemu. A lokacin yana yunkurin kai ‘ya’yansa hudu can sai aka ce za a hada da ni, amma sai mahaifiyata ba ta so hakan ba inda ta ce na yi karama a karshe dai aka fasa. Ta ce ya kamata a bar ni na kara girma, sai dai tafiyar da ba a yi ba ke nan domin daga baya mahaifinmu ya rasu.
Nasara
Babban burina na karantar daga dan ilimin da nake da shi don jama’a su karu su kuma yi amfani da shi a rayuwarsu, kuma ina da’awa a kauyuka ne saboda ta yi karanci a can. A yawanci kauyukan da nake zuwa da’awa sai na samu yawancin jama’ar ba su iya karatun fatiha ba. Nakan zubar da hawaye idan na koma wadansu kauyukan da na taba zuwa da’awa shekara goma da suka wuce, saboda a yanzu suna sanya hijabi sun iya karatun kur’ani, suna kuma gudanar da rayuwarsu bisa turbar da shari’a ta tanadar. Kullum ina addua’r Allah Ya amsa wadannan ayyukan da nake yi, idan har Ya amsa to na samu babbar nasara.
Shirin gidan rediyon bision Fm
Ai bision FM ne gidan rediyo na farko da na fara gunadar da shiri ba, kafin wannan lokacin na gudanar da wani shiri a gidan rediyon Najeriya (Radio Nigeria) a 1997. A lokacin suna shirin ‘Fadakarwa Ga Mata’. Na fara shirin ne da Malam Musa Yahaya. Maryam Gidado matar Sakataren Gwamnatin Tarayya lokacin Abaca ne ta dauki nauyin shirin, ta bukaci na rika gudanar da lacca da Turanci ga mata. Ta dauki nauyin shirin na tsawon wata uku. Daga baya ne muka fahimci ya kamata mu rika yi da Hausa domin amf anin matan da ba sa jin Turanci. Daga baya ne na ga abin da yawa sai na ga dacewar a samu wanda zai ci gaba da daukar nauyin. A nan ne Allah Ya hada ni da Hajiya Wada, inda ta dauki nauyi har tsawon shekara 5.
Lokacin hutu
Kusan kowane lokaci ina cikin gwagwarmayar rayuwa. A ranakun hutun karshen mako ma za ka samu ina gudanar da lacca ko da’awa ko kuma wadansu harkokin kasuwancina. Ina sayar da sabulu da turare da sauransu. Duk lokacin da nake bukatar hutu sai na kunna rediyona. Wani lokaci kuma na kalli talabajin.
Shawara ga ‘yan mata
A dangane da al’amarun aure, ina so kowane bangare; mata da mjii su sani suna da rawar da suke takawa domin aure ya zauna da kafafunsa, musamman ga miji wanda shi ne shugaba. Ya kamata miji ya sani akwai hakkoki matarsa da yawa a kansa da ya kamata ya sauke su, haka ya kamata mata ta fahimci yaya mijinta yake. Aure ya ginu a kan hakuri, fahimtar juna da kuma girmama juna. Idan aka samu wadannan to aure zai tsaya da kafafunsa.
Fatana
Burina Allah (SWT) ya amsa dukkan ayyukan da nake yi da suka hada da musuluntar da wadanda ba Musulmi ba da gina makarantun islamiyya da ba da sadakar abinci ga mabukata da gina kaburbura da sauransu.