Da dama daga cikin ’yan Najeriya sun kadu a kan tononin sililin da Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani ya yi game da yadda ake ba su makudan kudi duk wata a matsayin kudaden gudanar da ayyuka a mazabunsu. Wannan shi ne karo na farko da wani sanata ya fito fili ya bayyana irin kudaden da ake ba su don gudanar da ayyuka a mazabunsu. Haka wannan shi ne karon farko da Majalisar Dattawan ta tabbatar da batun na Shehu Sani.
Sanata Shehu Sani a kwanakin baya ne ya bayyana cewa ana ba kowane Sanata Naira miliyan 13 da rabi duk wata a matsayin kudin yin aiki a mazabarsa. Sanatan a lokacin da yake hira da manema labarai ya kara da cewa ana kuma ba kowane Sanata Naira dubu 700 a matsayin albashi a kowane wata. Sai dai Sanatan ya ce ba a tuhumar kowane Sanata kan yadda yake kashe albashinsa amma ana bukatar ya rika gabatar da bayanai dalla-dalla a kan yadda ya kashe Naira miliyan 13 da rabi a kowane wata.
Sanata Shehu Sani ya kara da cewa a kan ba kowane Sanata zunzurutun Naira miliyan 200 don yi wa mazabarsa aiki duk bayan wata uku. “Wata hukuma ce da ke karkashin Gwamnatin Tarayya take bukatar kowane Sanata ya gabatar da irin ayyukan da yake so a gudanar a mazabarsa, ba wai tsabar kudin ake damka musu a hannu ba. Ya ce hukumar ce za ta rika gudanar da ayyukan da sanatocin suka gabatar mata a rubuce a madadin sanatocin.”
dan Majalisar Dattawa Shehu Sani sai ya bayar da shawarar a soke makudan kudin da ake ba su duk wata da na duk bayan wata uku don gudanar da ayyuka a mazabunsu, a bar su da albashin da suke karba duk wata kawai.
A yayin da yake mayar da martani game da wannan batu, Shugaban Kwamitin Hulda da Jama’a na Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sahabi Abdullahi ya ce babu tantama game da batun da Shehu Sani ya fada wa duniya. Ya ce “ba a Majalisar Dattawa ce kadai hakan ke faruwa ba, hasali ma hakan na faruwa a sauran majalisun da ke fadin kasar nan da kuma a bangaren gwamnati, inda ya nuna nasu ne kawai ya fito fili.
Da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun yaba wa Sanata Shehu Sani a kan wannan tononin sililin da ya yi a majalisa. Alal misali Babban Lauya kuma dan rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya yaba wa Shehu Sani game da namijin kokarin fallasa abin da ’yan kasa suka dade suna zargi na biyan ’yan majalisar makudan kudade ba tare da sanin kowa ba. Ya ce zargin da Farfesa Itse Sagay ya yi a kwanakin baya cewa Sanatocin Najeriya sun fi takwarorinsu karbar kudi a duk fadin duniya, yanzu ya tabbata.
Idan aka yi la’akari da yadda ake da miliyoyin marasa aikin yi a kasar nan, da yadda ake fama da matsalar yunwa da tabarbarewar tattalin arziki, ba kowane Sanata Naira miliyan 13 da rabi duk wata a wannan yanayi ya zama abin takaici. Sannan idan aka dubi yadda wasu jihohi suka kasa biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 18 duk wata amma sanatocin suka kawar da kansu game da yadda ma’aikata da sauran ’yan kasa suke fuskantar tashin hankali, shi ma abin takaici ne.
Haka kuma abin takaici ne yadda ’yan majalisar da ya kamata a ce suna kare hakkin ’yan kasa ta hanyar yin dokokin da suka kamata, suka buge da azurta kansu a yayin da suka kyale sauran al’umma cikin talauci da tabarbarewar tattalin arziki.
Abin takaicin ma shi ne yadda babu wata hukuma da za ta rika tantance yadda sanatocin ke kashe Naira miliyan 13 da rabin da ake ba su duk wata ba, kamar yadda da yawa daga cikinsu suke gabatar da rasidan bogi game da yadda suke kashe kudaden a halin yanzu.