Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya zargi “makiya” da ruruta wutar zanga-zanga da bore a kasar a kokarinsu na yin juyin mulki wa gwamnatin Jamhuriyyar Musulunci a kasar.
Ya ce wadanda suke adawa da Tehran suna tunanin yin amfani da zanga-zangar su ruguza kasar.
- Hajjin 2022: Saudiyya ta sake sassauta dokokin kariyar COVID-19
- Isra’ila ta harba makami mai linzami filin jirgin saman Syria
Bayanan Shugaban Addinin suna zuwa zuwa bayan shafe makonni ana zanga-zanga a biranen kasar kan tsadar kayan abinci.
Rushewar wani dogon bene a watan jiya a Kudancin kasar ta dada zafafa zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin kasar.
Ayatollah Khamenei ya dade yana zargin takunkuman da Amurka ta sa wa kasarsa da jawo tashin gwauron farashin kayan abinci a kasar.
“Makiya suna fakewa da zanga-zanga don su kawo farmaki ga tsarin Musulunci,” ya bayyana haka a wani jawabi ga jama’ar kasar ta talabijin a ranar Asabar ta makon da ya gabata.
Ya ce: “Makiya suna son su tunzura jama’a su yi bore wa Jamhuriyyar Musulunci ta hanyar yakin tunani da kafafen Intanet da kudade da sojojin haya.”
“Amurkawa da mutanen Yammacin Duniya sun daba a kasa a baya, kan batutuwa da dama.
“Kuma har yanzu suna tunanin wannan hanya ce za su bi su sa mutanen Iran su yi adawa da Jamhuriyyar Musulunci,” inji shi.
Mutum 37 ne suka rasu bayan rushewar wani gini a mako biyu da suka gabata a birnin Abadan da ke Kudu maso Yammacin kasar a wani hadari mai muni da Iran ta gani a shekaru da dama.
An dora alhakin aukuwar hadarin a kan rashin ingancin aiki da rashin kula da kuma kauce wa ka’idojin gini.
Kuma mahukuntan kasar sun kama mutum 13 ciki har da Magajin Garin Birnin.
Sai dai duk da haka masu zanga-zangar sun fi dora wa shugabannin kasar laifi suna zarginsu da sakaci da kuma almundahana.
Rahotanni sun ce an ci gaba da yin zanga-zanga a sassan Iran, inda a wani bidiyo da aka sa a kafafen sadarwar zamani da ba a tantance ba aka ji wani na fadi da karfi cewa: “Allah Ya kashe Khamenei.”
Kuma an ji irin wannan daga murya a zanga-zangar birnin Bushehr mai tashar jiragen ruwa da ke Kudu.