Makarantar Kiwon Lafiya ta Sahlan da ke garin Jos a Jihar Filato, ta yi bikin yaye dalibanta da rantsar da sababbin daliban da ta dauka a karshen makon jiya.
Da yake jawabi a wajen taron Shugaban Gudanarwa na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Abdul Nasir Abdulmuhyi ya yaba wa makarantar bisa yadda take gudanar da ayyukanta.
Ya ce babu shakka ganin yadda aka tsara yanayin gudanar da makarantar, ya nuna cewa an yi kyakyawan tsari wajen koyar da dalibai harkokin kiwon lafiya. Daga nan ya yaba wa Gwamnan Jihar Filato, Barista Simon Lalong kan kokarin da yake yi wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
A jawabin tsohon Shugaban Karamar Hukumar Jos ta Arewa kuma tsohon dan Majalisar Wakilai na mazabar Jos da Bassa, Alhaji Sama’ila Muhammad Abdullahi ya ce makarantar tana da matukar muhimmanci ga al’ummar Najeriya baki daya, saboda fannonin kiwon lafiya da take koyarwa.
Ya ce ya kamata duk yaron da ya kammala makarantar sakandare, ya je ya karanta aikin jinya saboda muhimmancin da fannin yake da shi a tsakanin al’umma.
Ya yi alkawarin bai wa makarantar kyautar na’urorin gwaje-gwaje na zamani guda 20 da na’urorin kwanfuta guda 15 domin a sanya a dakin gwaje-gwaje na makarantar.
A jawabin Shugaban Sashin Koyar da Tsabtar Muhalli na Kwalejin Kiwon Lafiya ta Zawan da ke Jihar Filato, Mista Atangs Ishiku ya ce kokarin da shugaban makarantar ya yi wajen bude ta ya sanya suka taimaka wa makarantar wajen ganin ta mike da kafafunta.
Ya ce su ne suka fara zuwa suka yi wa daliban makarantar jarrabawa. Ya ce ganin irin kokarin da makarantar ta yi wajen cika ka’idoji, ya sanya aka yi mata rajista a matsayin makarantar koyar da kiwon lafiya.
Mista Atangs ya ce saboda rashin mayar da hankali kan harkokin kiwon lafiya ne ya sa ake samun matsaloli kan harkokin kiwon lafiya a kasar nan.
“A Najeriya ne kadai idan ka je shagunan sayar da magunguna za ka ga marasa lafiya sun yi layi ana ba su magani, wanda hakan bai kamata ba. Idan ka je asibitoci masu zaman kansu za ka ga wadanda ba su karanta aikin kiwon lafiya ba, suna duba marasa lafiya. Irin wadannan abubuwa suna kawo mana matsaloli kan harkokin kiwon lafiya a kasar nan,” inji shi.
Sai ya yi kira ga gwamnati ta kara kudaden da take warewa a kan harkokin kiwon lafiya. Kuma a rika karfafa wa kungiyoyi masu zaman kansu kan harkokin kiwon lafiya gwiwa.
Tunda farko a jawabin, Shugaban wannan Makaranta, Malam Muhammad Shafi’u Yakubu ya ce kalubalen da ake fuskanta a Arewa a bangaren kiwon lafiya ne ya karfafa musu gwiwar bude makarantar. Don horar da jami’an kiwon lafiya da za su rika yin aiki a asibitocin gwamnati da asibitoci masu zaman kansu.
Ya ce daga lokacin da suka bude makarantar zuwa yanzu al’ummar kasar nan sun fara cin gajiyarta ta fannoni daban-daban. “Mun samu nasarori da dama a makarantar, domin daga lokacin da muka bude ta a shekarar 2013 zuwa yanzu mun yaye dalibai 100. Zuwa yanzu muna da dalibai 150 da suka fito daga jihohi daban-daban na kasar nan. Wata babbar nasara da muka samu ita ce a cikin sababbin daliban da muka dauka a bana, har da wani Farfesa da ya zo zai yi karatu a makarantar,” inji shik