✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Farfesa Ango ta kasa nuna yara 101 da aka ce Zango ya dauki nauyin karatunsu

Bayan da kafafen sadarwa suka ce fitaccen jarumin nan Adam A. Zango ya dauki nauyin karatun yara 101 a  makarantar  Farfesa Ango Abdullahi da ke…

Bayan da kafafen sadarwa suka ce fitaccen jarumin nan Adam A. Zango ya dauki nauyin karatun yara 101 a  makarantar  Farfesa Ango Abdullahi da ke Zariya, makarantar ta kasa nuna daliban inda Shugaban Makarantar kuma ya ce ba ya gari.

Shugaban Makarantar Dokta Aliyu ya ce a jiya Alhamis da rana yana tare da shi wanda ya dauki nauyin karatun yaran a Sakkwato, donn haka a yi hakuri idan ya dawo zai kira wakilinmu domin ganin daliban.

Da wakilinmu ya shaida masa cewa ana zargin labarin ba gaskiya ba ne, sai ya ce to duk abin da ake so a rubuta domin Adamu Zango ba dan Zariya ba ne kuma bai san kowa ba dama ya ba da tallafin ne ga yara 100 ya ce a dauka kuma a raba tallafin kamar haka: “Mun ba Mai martaba Sarkin Zazzau guda 40 sai Jam’iyyar PDP 40 , Jam’iyar APC 40, ka ji yadda muka raba tallafin. Don haka idan Allah Ya sa na dawo zan kira domin mu tara maka yaran ka gansu da idonka,” inji shi.

Da Aminiya ta tuntubi Alhaji Abubakar Ladan Ciroman Shantalin Zazzau ta waya domin jin gaskiyar cewa an ba su tallafin dalibai  40 a makarantar Farfesa Ango Abdullahi wanda Adamu A Zago ya bayar, sai ya ce a saninsa makarantar na ba su tallafin dalibai duk shekara amma bai sani ba ko akwai na Adamu Zango a ciki ba.