✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Dutse Standard ta yi bikin baje kolin fasahar dalibai 

Makarantar Dutse Standard ta yi bikin baje kolin fasahar daliban makarantar inda daliban suka gabatar da kayayyakin da suka sana’anta da suka hada da jakankuna…

Makarantar Dutse Standard ta yi bikin baje kolin fasahar daliban makarantar inda daliban suka gabatar da kayayyakin da suka sana’anta da suka hada da jakankuna da huluna da takalma da zane-zane da sauran kere-kere.

Sai kuma iyaye da malaman makarantar suka sayi kayayyakin da daliban suka yi domin kara musu karfin gwiwa.

Hajiya Bilkisu Goggo Shehu ita ce Shugabar Makarantar, ta ce sun bullo da shirin ne da nufin bunkasa basirar yara masu kwazo kasancewar wadansu yaran ba su da hazaka wajen karatu  amma suna da basira a zane-zane, yayin da wadansu kuma Allah Ya hada musu duka.

Hajiya Goggo ta ce ta yin haka ne za su samar da yara masu hazaka a bangarori da dama wadanda za su koyi sana’ar da za su rike kansu kafin su kai ga shiga jami’a saboda yanzu aikin gwamnati ba kowa ke samu ba.

Hajiya Goggo ta shawarci iyayen yara su rika kara wa yaransu karfin gwiwa domin ta haka ne iyayen za su gano irin basira da kwazon da ’ya’yansu ke da su ba sai karatu kadai ba.

Ta ce burinta shi ne su ankarar da gwamnati cewa lokaci ya yi da za a rika koya wa yara sana’a tun daga firamare a daukacin makarantun gwamnati da ke jihar domin su zamo masu dogaro da kansu nan gaba.

Da yake jawabi a wajen bikin, tsohon dan Majalisar Jihar Jigawa mai wakiltar Karamar Hukumar Taura, Alhaji Rabi’u Dangabi Kwalam ya ce tsarin da makarantar ta fito da shi abu ne mai kyau kuma kamata ya yi dukkan makarantun gwamnati su yi koyi da ita.

Shugabar Kungiyar Iyaye da Malaman Makarantar Hajiya Rukayya Bello cewa ta yi idan gwamnati za ta ba bangaren kirkira da fasaha kula ta musamman tun daga firamare, za a samu yaran da za su taso nan gaba masu basira iri-iri da kasar nan za ta yi alfahari da su.