✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Bethel: An sako karin dalibai 10

Dalibai 100 ke nan aka sako, saura 21 a hannun masu garkuwa.

An sako karin mututm 10 daga cikin dalibai 121 da ’yan bindiga suka sace a makarantar sakandaren Bethel Baptist da ke Jihar Kaduna.

Wani babban jami’in makarantar ya tabbatar cewa an sako daliban ne bayan an biya kudin fansa, tuni kuma aka mika su ga iyayensu domin a duba lafiyarsu.

Ya ce an sako daliban su 10 ne a ranar Asabar, kwana 75 bayan ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar sun yi won gaba da su daga makarantar da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna .

Kawo yanzu dai mutum 100 ke nan daga cikin daliban ’yan bindigar suka sako, ragowar 21 kuma na tsare a hannunsu.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto dai hukumomin jihar ba su ce komai ba.