Makarantar Alfurkan International da ke garin Jos a Jihar Filato ta yi bikin yaye dalibanta karo na 6 tare da kaddamar da gidauniyar neman gudunmawar gina mazauninta na dindin, a ranar Lahadin da ta gabata, a dakin taro na babban masallacin Jos.
Da yake jawabi a wajen taron, Malam Imam Ahmad Adam Kutubi ya bayyana matukar farin cikinsa da kokarin da wannan makaranta take yi. Ya yi kira ga daliban da aka yaye da su ci gaba da neman ilmi a manyan makarantu na gaba. Ya ce suna son a sami likitoci da lauyoyi da sojoji da ’yan sanda da ’yan kasa nagari a cikinsu.
A nasa jawabin Walin Sarkin Sharifan Sakkwato kuma shugaban kamfanin mai na Sahabi, Malam Alkasim Sahabi ya yi kira ga iyayen yara da su kara dagewa kan tsayawa yaransu wajen neman ilmi, ta hanyar biya masu kudaden makaranta da dukkan abubuwan da suke bukata a makarantu.
Shi ma a nasa jawabin, Malam Mansur Sulaiman cewa ya yi manzon Allah (saw) ya ce mafi alheri a cikin al’ummar Musulmai, shi ne wanda ya karance Alkura’ani kuma ya karantar da shi. Ya ce duk mutumin da ya ba Alkura’ani muhimmanci Allah zai daukaka darajarsa.
Tun da farko a nasa jawabin, Daraktan makarantar, Malam Sahailu Ahmad Kutubi ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne don yaye dalibansu karo na 6, da suka sauke Alkura’ani da fanni boko tare kuma da kaddamar da gidauniyar neman gudunmowar gina mazaunin wannan makaranta na dindindin.
Ya ce a cikin daliban da suka yaye akwai na bangaren karamar makarantar sakandire guda 40 da na bangaren firamare guda 50 da kuma na bangaren haddar Alkura’ani mai girma. Ya ce daga lokacin da aka bude wannan makaranta zuwa yanzu sun yaye dalibai sama da 700. Ya yi kira ga masu hanu da shuni da su rika tallafa wa irin wadannan makarantu.