✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Makaranta ta yaye mahaddatan Kur’ani 53 a Gombe

Wannan ne dai karo na bakwai da makarantar ke bikin yaye daliban.

Makarantar Kimiyyar Kur’ani mai suna AQSAT a Jihar Gombe ta yaye dalibai 53 da suka haddace Alkur’ani mai girma.

Wannan dai shi ne karo na bakwai da makarantar ke bikin yaye daliban.

Da yake jawabi a wajen taron Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa, ya taya daliban murnar saukar karatun, inda ya ce ba kowa Allah yake ba baiwar haddace Kur’ani ba.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Masana’antu da Cinikayya na Jihar, Nasiru Aliyu, ya ja hankalin su da cewa su mayar da hankali kan karatun da suka yi.

Wasu mahaddata mata da aka yaye a makarantar

Ya kuma hore su da su rike Kur’ani da hannu biyu dan ya cece su a ranar Lahira.

Daga nan sai ya jinjina wa malaman makarantar bisa jajircewarsu wajen koyar da dalibai suka kuma dora su a tafarki nagari.

Shi ma a nasa jawabin shugaban Makarantar Ustaz Auwal Abdullahi, Gafakan Akko kuma Gonin Gombe, kiran daliban da aka yaye ya yi da su yi amfani da ilimin da suka koya, yana mai cewa matsalar kasar nan ita ce rashin aiki da abin da aka koya.

Gafakan Akko, Wanda mai bai wa Gwamnan Gombe shawara ne kan alaka da al’umma ya wakilta ya ce dabi’ar su da tarbiyar su ta zama fiye da na wadanda basu karanta Kur’ani ba.

A cewarsa, duk shekara ana samun ci gaba a makarantar domin har daga wasu Jihohin da ma kasar Kamaru iyaye su kan kawo ’ya’yan su karatu a makarantar.

Mai Martaba sarkin Pinda Alhaji Seyoji Ahmad, addu’a da fatan Alkairi ya yi wa daliban da suka haddace Kur’anin sannan ya yaba wa iyayen su bisa kokarin su na tura yaran nasu karatu.

Aminiya ta gano cewa makarantar, wacce aka kafa kimanin shekara 12 da suka gabata ta ya ye fiye da dalibai 350 da suka haddace Kur’ani mai girma.