An gurfanar da wani makaniken mota a gaban wata Kotu da ke zamanta a yankin Karu a jihar Nasarawa kan zarginsa da satar wayar wani makwabcinsa.
Rundunar ’yan sandan Jihar ce ta gurfanar da makaniken mai shekaru 30 wanda mazauni ne a yankin da Kotun ke zamanta.
- ‘Babu bukatar shaidar gwajin COVID-19 daga wurin dalibai yayin komawa makaranta’
- Mutum miliyan 15 na ta’ammali da kwaya a Najeriya — Buba Marwa
Sai dai Makaniken kememe ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi na zargin sibaran-na bayye.
Jami’in dan sandan da ya gabatar da wanda ake kara a gaban kotun, Ayotunde Adejanyi, ya bayyana cewa ana tuhumar makaniken da aikata dan hali na satar wayar salula da wani makwabcinsa da suka zama wuri guda.
Ya ce abokin zaman makaniken ne ya kai musu korafi caji ofis tun a ranar 13 ga watn Dasimbar 2020, inda ya labarta masu cewa ya nemi wayarsa da ta budurwa ya rasa bayan ya farka daga barci kuma yana zargin abokin zaman nasa ne ya yi layar zana da su.
Mista Adejanyi ya ce laifin da ake zargin makaniken da aikatawa ya saba wa sashe na 288 cikin kundin dokokin aikata miyagun laifuka.
Bayan sauraron kowane bangare, Alkalin kotun Mai Shari’a Anas Isa, ya bayar da belin wanda ake tuhumar kan kudi N100,000 tare da gindaya sharadin gabatar da mutane biyu wadanda za su tsaya masa ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 9, ga watan Maris na 2021.