Majalisar Dokokin Jihar Yobe ta yi fatali da rade-raden tsige Gwamna Mai Mala Buni a wani zama da ta yi na karyata batun wanda kuma ta kada kuri’ar amincewa da gwamnan.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Potiskum ta Tsakiya wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Yada Labarai na majalisar, Abdullahi Adamu Bazuwa ne ya sanar da hakan a wata hirarsa da manema labarai a dakin taro na majalisar.
- Mutumin da ya siyar da dansa da matarsa ya shiga hannu
- Batanci: Tambuwal ya cire dokar hana fita a Sakkwato
A cewarsa, “mambobin majalisar sun yaba da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Majalisar Dokokin da bangaren zartarwa na gwamnati a jihar”.
“Haka zalika Mambobin sun yaba da kokarin dukkanin hukumomin tsaro a jihar domin samun zaman lafiya a jihar.
“Haka kuma muna yin Allah wadai da labarin da aka wallafa a wata kafar yada labarai ta intanet, THE NEWS NET GLOBAL mai taken Yunkurin Tsige Gwamna Buni kan kin ba da tikitin takara ga ‘yan majalisar Yobe 18 cikin 24.
Honarabul Bazuwa ya ce majalisar ta kuma yi da fatali da wani hoton bidiyo da wani Mohammed Yakubu Lai ke yadawa a kan batu tsige gwamnan.
“Mu duka ’yan majalisar muna bayyana cewa wannan magana karya ce, marar tushe da kuma an yi ta ne da mugun nufi.”
“A halin yanzu, muna son kara jaddada goyon bayanmu da hadin kai ga Mai girma Gwamna Mai Mala Buni saboda mutuntawa da kyakkyawar alakar da ke tsakanin bangarorin gwamnati biyu”.
“Daga karshe, mun kulla niyyar daukar matakin shari’a a kan wadanda suka aikata wannan aika-aika domin dakike aukuwar hakan a gaba.”