✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Wakilai za ta tsunduma yajin aiki saboda matsalar tsaro

Majalisar ta yi barazanar shiga yajin aiki har sai an tabbatar da tsaron rayukan al'umma.

Majalisar Wakilai ta yi barazanar tsunduma yajin aiki kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a fadin Najeriya.

Dan majalisar mai wakiltar Karamar Hukumar Fagge daga Jihar Kano, Honarabul Aminu Sulaiman Goro ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis, inda ya tabbatar da cewa koyaushe suna samun rahoton hare-hare da ‘yan bindiga ke kaiwa.

Honorabul Goro ya ce kusan ko yaushe sai sun tafka muhawara saboda yadda matsalar tsaron ta fi tabarbarewa a Arewancin Najeriya.

Ya ce al’amura sun lalace fiye da yadda ake tsammani, sakamakon yadda ake kashe tare da satar mutane ba ji ba gani a kullum.

Sai dai ya ce harin bam din da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya munana, saboda tuni aka hana mutane bin tituna saboda gudun kai musu hari.

”Wannan ya nuna cewa an kama sama an kama kasa gashi nan dai, to ban san me suke so su yi ba.

“Mu a matsayinmu na ‘yan majalisa mun ga cewa dukkan abin da gwamnati ta nema na harkar kasafin kudi ko doka, ba mu taba bata lokaci ba muna amincewa, to amma kullum masifar nan kara ta’azzara take.

“Muna ganin kamar jama’ar da muke wakilta sun fara gajiya, ba wai iya gwamnati ba, har mu kanmu.

“Duk abin da za mu yi mun yi don ganin an inganta harkar tsaro, to amma kullum jiya a yau, don haka muka ga cewa lallai-lallai ya kamata mu yi wani abu daban, mu rufe majalisa mu tashi.”

Ya kara da cewa, “Za mu tashi har sai jami’an tsaro sun zo sun gaya mana mene ne ya ke faruwa? kuma menene za su yi?, sannan idan sun gaza me suke bukatar mu yi musu?”.

Goro ya ce a wasu lokutan suna da masaniyar abubuwan da gwamnati ke yi amma a wasu lokutan ba su san me take aikatawa ba.

“Don haka idan mu ma za mu bi sahun ASUU ne, mu ma mu shiga yajin aiki, gara mu rufe mu tafi har sai an tabbatar mana da cewa jama’ar da suka turo mu wakilci, lafiyarsu da dukiyarsu da kuma rayukansu za su zamanto cewa an kare su.”

Wannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan harin bam da ‘yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya yi sanadin salwantar rayukan wasu tare da jikkata wasu, yayin da kuma maharan suka sace wasu da dama.

Harin ya fusata al’ummar Najeriya da dama, inda wasu ke ganin gwamnati ba ta tabuka komai ba kan kare rayukan wanda suka rasu a harin, duba da yadda ‘yan bindigar suka sha yunkurin farmakin jirgin a baya.