✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Wakilai ta kafa Kwamitin Tsaro na Musamman

Kwamitin zai lalubo mafita tare da bayar da shawarwarin hanyoyin samun nasara a bangaren tsaro.

Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin tsaro na musamman mai mambobi 40 a sakamakon karuwar matsalar tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Majalisar ta umarci kwamitin da ya gabatar da ya lalubo mafita tare da bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a yi nasarar a bangaren tsaron kasar.

Kwamitin ya kunshi dukkanin manyan shugabannin Majalisar guda 10 da sauran ’yan Majalisar guda 30.

Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan yayin zamanta na ranar Laraba.

Ya ce kwamitin zai gabatar da rahotonsa nan da makonni uku sannan a tura shi ga bangaren zartarwa.