✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Tsige Duk Sarakunan Jihar Kano —Majalisa

Jihar Kano ta wayi gari babu Sarki bayan majalisar dokoki ta soke duk masana'antun jihar

Majalisar Dokokin Kano ta tsige Sarkin Kano Aminu Sarkin Kano Aminu da sauran sarakuna hudu da ke fadin jihar.

Majalisar sanar da haka ne bayan ta amince da rushe masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin jihar ta Abdullahi Ganduje ta samar.

Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Chediayar Yan Gurasa mai wakiltar karamar hukumar Dala ya sanar bayan zaman cewa, daga “yanzu, babu sarki a Jihar Kano har sai gwamna ya amince da naɗa wani sabon.”

Ya ci gaba da cewa: “Dokar da aka yi yau ta soke wadannan kirkirarrun masarautu guda biyar.

”An dawo da darajar Kano yadda take tun zamanin Shehu Usmanu Danfodiyo bayan jihadi.

“Yanzu [Jihar] Kano za ta zama da  sarki guda daya, idan gwamna ya sa hannun a kan dokar, an rushe wadannan masarsutun babu su,” in ji Chediyar ’Yan Gurasa.

Wasu bayanai na nuni da cewa an kira zaman majalisar masu nadin sarki domin fara aiki gabanin mika wa gwamna sunan wanda zai kasance Sarkin Kano.

Majalisar ta kuma umarci hakiman da gwamnatin Ganduje ta daga darajarsu zuwa sarakuna a masarautun da abin ya shafa  cewa su koma matsayinsu na da.

Haka kuma ta umarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya yi duk abin da ya kamata domin mayar da Masarautar Kano yadda take kafin a mayar da su zuwa biyar.

Masarautun da hakan ta shafi sarakunansunsu ne na Kano, Aminu Ado Bayero; Bichi, Nasiru Ado Bayero; Gaya, Karaye da kuma Rano.

Masarautun da hakan ta shafi sarakunansunsu ne na Kano, Bauchi, Gaya, Karaye da kuma Rano.

Hakan ta faru ne washegarin da majalisar ta fara karatu kan kudirin yi wa dokar masarautun jihar da gwamnatin Ganduje ya samar gyaran fuska a ranar Laraba, inda a ranar Alhamis aka yi karatu na biyu da na uku, samman ta amince.

A halin yanzu ana jiran make ta mika dokar ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin rattaba hannu.

Aminiya ta ruwaito cewa an girke jami’an tsaron hukumar DSS a Fadar Sarkin Kano a safiyar Alhamis da ake soke sabbin masarautun.