Majalisar Tarayya ta roki masu fada a ji da su sa baki domin ganin an kawo karshen zanga-zangar #EndSARS da ke ci gaba da haifar da asara a sassan Najeriya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi rokon ne bayan samun bayanin halin da ake ciki sakamon kazancewar zanga-zangar daga shugaban ’yan sanda da na DSS.
- EndSARS: An janye ’yan sanda masu kare manyan mutane
- ‘Ya kamata Sarkin Musulmi ya hana yin kayan aure’
“Dukkannin shugabanni ba tare da la’akari da bambancin siyasa, addini ko yanki ba, dole ne mu mike domin ganin an tsayar da wannan bore.
“Yanzu abin ya rikide ya koma wani abu sabanin aikin manufar neman soke rundunar SARS”, inji shi.
Ya ci gaban da cewa, “masu yawon cewa suna zanga-zangar sun nuna karara cea ba su da wata alaka da ainihin #EndSARS.
“Ina kira ga dukkannin masu fata na gari da cewa wajibi ne mu nuna kishi domin dorewar zmaan lafiya a wannan kasa kuma komai na tafiya daidai.
“Mutane na da ‘yancin sukar abin da bai yi daidai ba ta halastattun hanyoyi da suka hada da zanga-zangar lumana.
“Amma kar mu bari a karkatar da mu zuwa tayar da hankula kamar yadda ake yi a wasu sassan kasar”, in Shugaba Majalisar.
Ya shaida wa ‘yan jarida cewa “Muna tuntubar sauran ’yan Majalisa, bangaren zartarwa da sauran jama’a kan hanya mafi dacewa ta magance wannan matsala.
Ya jaddada cewa “Ba ma goyon bayan duk wani nau’in zanga-zanga na tashin hankali. Mun yi amanna cewa an faro zanga-zangar #EndSARS da ikhlashi da kishin kasa da nufin ganin an yi sauyi nan take’’.