Majalisar riƙon ƙwarya ta Gwamnatin Mali ta ƙara wa Shugaban Mulkin Sojin ƙasar, Janar Assimi Goita, wa’adin mulki na shekara biyar, wanda za a iya sabunta shi fiye da sau daya ba tare da zaɓe ba.
A bara ne Janar Goita ya yi alƙawarin maido da mulkin dimokuradiyya a ƙasar, sai dai hakan ba ta samu ba.
Wannan matakin ya bude hanya ga Janar Goita ya ci gaba da jagorantar kasar ta yammacin Afirka har zuwa aƙalla shekarar 2030, duk da alƙawarin da gwamnatin sojan ta yi na komawa mulkin farar hula a watan Maris na shekarar 2024.
Sai dai sabon ƙudirin dokar ya yi tanadin cewa Goita zai ci gaba da mulki har zuwa lokacin da ƙasar za ta daidaita.
Majalisar riƙon ƙwaryar wadda ke da mambobi 147, ce ta amince da ƙudirin, kuma yanzu yana jiran Janar Goita da kansa ya sa hannu domin ya zama doka.
A 2021 ne Janar Goita ya hau karagar mulkin ƙasar a wani juyin mulkin soji, inda ya alƙawarta magance tashe-tashen hankulan masu iƙirarin jihadi.
Sai dai har yanzu mayaƙan na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare, inda a baya-bayan nan ma suka kai hare-hare kan sansanonin sojin ƙasar tare da kashe sojoji masu yawa ciki har da sojojin hayar Rasha