An samu baraka a Majalisar Malaman Jihar Kano, kasa da awa 24 bayan ta sanar da dakatar da shugabanta, Sheikh Ibrahim Khalil, kan zargin ci da addini.
A ranar Litinin Majalisar ta sanar da nadin Farfesa Abdallah Pakistan a matsayin shugabanta na riko, bayan ta dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil, wanda ta zarga da neman siyasantar da ayyukanta da kuma amfani da ita wajen neman biyan bukatun kashin kansa.
- An nada Farfesa Saleh Pakistan Shugaban Majalisar Malaman Kano
- An cire wuka da ta shekara 26 a kan wani mutum
A ranar Talata, gamayyar Majalisar Malamai da kungiyoyin Musulunci a Jihar Kanon sun fito suna nesanta kansu da sanarwar dakatarwar.
A sanarwar da Sakataren gamayyar, Dakta Ahamad Dukawa, ya sanya wa hannu, malaman sun bayyana cewa ba da yawunsu aka tsige Sheikh Ibrahim Khalil ba, kuma ba sa goyon bayan tsige shi.
Sanarwar ta yi gargadi cewa cire malamin na iya kawo rabuwar kan al’ummar Musulmi, su kuma ba sa kaunar ganin hakan.
Malaman sun kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata damuwa ba, cewa za su shawo kan matsalar.
Manyan malaman da suka sanya hannu a dakatar watsi da tsige Sheikh Ibrahim Khalil sun hada da: Sheikh Karibullah Sheikh Nasiru Kabara, Sheikh Abdulwahab Abdallah da Dakta Bashir Aliyu Umar.
Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo, Farfesa Mohammad Babangida Mohammad, Imam Nasiru Mohammad Adam da kuma Dakta Bashir Mu’azzam Mai Bushira.
Da ma dai tun a lokacin da Majalisar take gudanar da taron dakatar da Sheikh Khalil, wasu mahalarta taron suka nuna rashin amincewarsu da hakan.