‘Majalisar Malamai ta Najeriya’ ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya janye takunkumin da ya sa wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara tare da bude masallacinsa.
Mukaddashin Shugaban Majalisar kuma jagoran Darikar Tijjaniya, Sheikh Dan’azumi Tafawa Balewa ne ya yi kiran yayin zantawa da manema labarai a gidansa a ranar Alhamis, a Bauchi.
- Kotu ta bayar da belin Mahdi Shehu
- Bana shakkar faduwa zabe a 2023 –Makinde
- Mahara sun kashe matashi, sun dauke mahaifiyarsa a Jigawa
- Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan wata shida a Dubai
“Wannan hakki ne da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya samar wa kowa, kuma ya yi daidai da koyarwar Alkur’ani Mai Girma, inda Allah Yake cewa, ‘Babu tilastawa a addini’.
“Muna mutunta duk wani sabanin ra’ayi da aka samu, kuma a shirye muke da mu zauna da duk wata darika don fahimtar juna,” cewarsa.
Ya ce, ya kamata Ganduje ya kyale Abduljabbar ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullun domin yi masa adalci kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane dan kasa ’yancin yin addini.
A cewarsa, shirya mukabala da Ganduje ya yi tsakanin Abduljabbar da wasu malamai abu ne mai kyau, amma an samu tsaiko tunda kotu ta dakatar da yin hakan.
Malamin ya kara da cewa majalisar an kirkireta tun a shekarar 1980, kuma a shirye take wajen shirya zama da dukkanin bangarorin dariku da ke Najeriya don fahimtar juna tare da yin tafiya daya.
“Don haka muna rokon Ganduje, kwararren dan siyasa da muke ganin girmansa da ya yi koyi da koyarwar Alkur’ani Mai Girma, da kuma umarnin Allah a matsayinsa na shugaba da ya yi adalci a dukkanin lamuransa,” inji shi.