✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Malamai ta karrama Garba Satatima kan bunkasa ilimin manya

Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta karrama fitaccen malamin nan Dokta Garba Babanladi Satatima bisa guddunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa harkar ilimin manya da…

Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta karrama fitaccen malamin nan Dokta Garba Babanladi Satatima bisa guddunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa harkar ilimin manya da aka fi sani da yaki da jahilci a Jihar Kano.

A kwanakin baya ma Jami’ar Ibadan ta karrama Dokta Garba Satatima bisa guddunmawar da yake bayarwa ga harkar ilimin manya a fadin kasar nan.

A jawabin Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya ce majalisar ta shirya wannan karramawa ce don yabawa ga abin da  Barden Madaki yake yi ga harkar ilimin manya a fadin jihar. “Kowa yana sane da irin gudunmawar da Babanladi yake bayarwa wajen bunkasa ilimi musamman ilimin manya lura da cewa ya riga gwamnati fara bude makarantar yaki da jahilci a Jihar Kano. Domin ya bude tasa tun a shekarun 1960. Don haka daga wannan lokaci zuwa yau Allah ne kadai Ya san yawan mutanen da suka amfana daga gare shi.Kuma sanin muhimmancin da ilimi yake da shi ga al’umma ya sa muka ga akwai bukatar mu gimama duk wanda ya yi wa harkar ilimi hidima kamar Babanladi,” inji shi.

Sheikh Ibrahim Khalil ya yi kira ga jama’a su yi koyi da Dokta Babanladi Satatima wajen amfanar da mutane ’yan uwansu.

A jawabin, Dokta Garba Satatima ya bayyana godiyarsa ga Majalisar Malaman bisa wannan karramawa da ta yi masa tare da yaba wa wadansu fitattun mutane wadanda a cewarsa sun bayar da guddunmawa wajen taimaka wa kafuwa da bunkasar makarantar tasa. “Ina godiya mai dimbin yawa ga wadanda suka shirya wannan taro. Haka ba zan manta da marigayi Sarkin Kano Alhaji Dokta Ado Bayero ba, bisa irin gudunmawar da ya ba mu tun daga lokacin da muka kafa wannan makaranta har ya rasu. Ina kuma godiya ga wadansu daidaikun mutane wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban wannan harka,” inji Satatima.