✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar kasa ta amince da Naira dubu 27 mafi karancin albashi

Majalisar kasa ta Najeriya ta amince da tsayar da Naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi. Yayin da Majalisar ta kuma amince…

Majalisar kasa ta Najeriya ta amince da tsayar da Naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi. Yayin da Majalisar ta kuma amince da Naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.

A yau Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar a fadarsa wadda ta kunshi tsofaffin shugabanni da tsofaffin alkalan alkalan Najeriya da kuma gwamnoni da shugabannin majalisa.

Ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige ya bayyana cewa, za a mika kudirin ga majalisa a ranar Laraba domin amincewar ta.