Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudurin gyara masarautu na shekarar 2019 zuwa doka yayin zamanta na gaba.
Babban Sakataren Yada Labarai na majalisar Uba Abdullahi ya ce an amince da kudirin ne a zaman babban zauren majlaisar.
- An dawo da ’yan Najeriya 104 da suka makale a Chadi —NEMA
- Buhari ya ziyarci kabarin Manzon Allah (SAW)
Ya ce majalisar ta kuma samu wasika daga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta neman tabbatar da Mahmoud Balarabe a matsayin shugaban hukumar korafe-korafe da Yaki da Rashawa ta jihar mai cikakken iko.
Abdullahi ya bayyana cewa majalisar ta mika batun kwamitinta na yaki da rashawa domin ci gaba da aiki a kai.
Gwamnan ya kuma aiko wa majalisar da daftarin kudirin kafa hukumar kula da hanyoyin karkara, wanda majalisar ta mika ga kwamitin da ya dace domin ci gaba da daukar matakai.
Majalisar ta kuma samu wasikar gwamnan da ke bukatar fara amfani da Taken Jihar Kano wanda gwamnatin jihar da Jami’ar Bayero suka tsara.
Gwamnan ya kuma turo da daftarin dokar mallakar fili domin tattaunawa da amincewar majalisar.
Sauran bukatun sun hada da na neman nada Balarabe Hassan Karaye a matsayin shugaban hukumar zabe ta jihar da kuma dokar adashen gata na inshorar lafiya.