Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da bukatar Gwamna Abdullahi Ganduje na karbar rancen Naira biliyan 20 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) ta hannun Bankin United Bank for Africa (UBA).
A zamanta na ranar Litinin, Shugaban Majalisar, Abdulazeez Garba Gafasa, wanda ya karanta wasikar gwamnan, ya ce bashin kayayyakin aikin yana da kashi tara na kudin ruwa da za a biya cikin shekara 10.
- Yadda ’yan sanda ke ‘garkuwa da mutane’ a Kano’
- ‘Ayyukan ta’addanci na karuwa a Kano’
- ’Yan jarida za su karrama fitattun ’yan Najeriya 7 a Kano
- Hisbah ta hana ‘Black Friday’ a Kano
Ya ce rancen zai dace da yunkurin jihar na sake fasalin tattalinta da annobar COVID-19 ta lalata.
Gwamna Ganduje a cikin wasikar, ya ce ya fada wa masu ruwa da tsaki cewa an samu sauyin tattalin arziki tun a shekara ta 2016.
Shugaban Masu Rinjaye, Kabiru Hassan Dashi, ya bukaci Majalisar ta yi la’akari da bukatar ta gwamnan, saboda kalubalen da kasuwar Kano ta samu sakamakon tabarbarewar yanayin tattalin arziki.
Ya ce an amince da rancen ne don cike gibin matsalar tattalin arziki da annobar COVID-19 ta haifar.
Bayan tattaunawa, Majalisar ta amince baki daya da bukatar.