Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da naɗin sabbin Kwamishinoni da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya zaɓa su zama mambobin majalisar zartarwa ta jihar.
Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ne, ya sanar a ranar Talata cewa ’yan majalisar sun amince da sunayen ne bayan tattaunawa a zamansu.
- Kisan Gombe: Majalisa ta umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki
- Uba Sani ya mayar wa iyalan Abacha filayen da El-Rufai ya ƙwace musu
Da farko, gwamnan ya aike da sunayen mutane shida a ranar Litinin.
Daga baya ya sake aike ƙarin sunan Nura Iro Ma’aji, wanda majalisar ta ƙara sannan ta tabbatar da su.
Daga cikin waɗanda aka tabbatar akwai Shehu Wada Sagaji, tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin, wanda aka cire daga muƙaminsa a ranar Alhamis da ta gabata.
Sauran sun haɗa da Abdulkadir Abdulsalam, Gaddafi Sani Shehu, Ibrahim Wayya, Dokts Dahiru Hashim Muhammad, da Dokta Ismail Aliyu Dannaraya.
Wannan matakin zai bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf damar kammala kafa majalisar zartarwarsa.
Sabbin kwamishinonin, ana sa ran za su taimaka wajen aiwatar da manufofin gwamnan domin inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.