✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Kano ta samu sabon shugaba

A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zabi Alhaji Isyaku Ali danja daga mazabar Gezawa a matsayin sabon shugaban majalisar,…

A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zabi Alhaji Isyaku Ali danja daga mazabar Gezawa a matsayin sabon shugaban majalisar, sakamakon murabus din da tsohon Shugaban Majalisar Alhaji Gambo Sallau ya yi.  An zabi sabon shugaban ne bayan gabatar da kudirin haka daga Alhaji Abdu A. Abdurrahman daga mazabar Minjibir da kuma goyon bayan haka daga wakilin mazabar Warawa, Labaran Audu. Alhaji Gambo Sallau ya aika wa majalisar takardar murabus daga shugabancin ne bisa hujjar ba zai iya barin Jam’iyyar PDP ba, wadda ta rasa rinjaye a majalisar sakamakon canja sheka zuwa APC da wakilan majalisar 26 daga cikin 32 suka yi a ranar Litinin da ta gabata. Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnoni hudu na Jam’iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a bara, yayin da akasarin ’yan majalisar tarayya daga jihar suka fice daga PDP zuwa APC, bisa cewa PDP ba ta da adalci.