✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da mambobinta biyar

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da mambobinta biyar sakamakon rigimar da ta barke a majalisar a cikin makon da ya gabata. Yayin da yake…

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da mambobinta biyar sakamakon rigimar da ta barke a majalisar a cikin makon da ya gabata.

Yayin da yake sanar da batun dakatarwar ga membobin majalisar, bayan dawo da zama da majalisar ta yi ranar Litinin Shugaban majalisar Abdul’azeez Garba Gaffasa, ya bayyana cewa an dakatar da mambobin majalisar ne saboda rashin da’a da kuma karya dokokin majalisar.

Mambobin majalisar da aka dakatar sun hada da: Honorabul Garba Ya’u Gwarmai wakilin al’umar Kunchi da Tsanyawa sai Labaran Abdul Madari Mai wakiltar Warawa. Haka kuma an dakatar da Isiyaku Ali Danja wakilin Gezawa da kuma Mohammed Bello wakilin mazabar Rimin Gado da Tofa. Sai kuma Honorabul Salisu Ahmed Gwangwazo wakilin Birni da Kewaye.

A cewar Shugaban Majalisar “An dakatar da membobin Majalisar biyar ne, saboda karya dokokin majalisar, inda suka hargitsa zaman majalisar tare da hana ci gaba da gudanar da ayyukan majalisar wanda ya saba da dokar majalisar ta IV sashi na 4 a, b,, d da kuma e.

Cikakken rahoton na nan tafe.