✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisar Dokokin Kano ta bai wa Ganduje damar karbo bashin N10bn

Za a dasa na'urori don ingata sha'anin tsaro a Jihar

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince tare da bai wa Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, damar ciyo bashin Naira biliyan 10 don saka kyamarorin tsaro na CCTV a Jihar.
Amincewar ciyo bashin ta biyo bayan takardar da Gwamnan ya aike wa majalisar, wadda shugabanta, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta a zauren majalisar yayin zamanta na ranar Laraba.
Ganduje, ya ce za a sanya na’urorin ne la’akari da barazanar tsaro da Jihar ke fuskanta musamman a baya-bayan nan.
Majalisar ta amince bayan tattauna batun tare da bada shawarwari da ‘yan majalisar suka yi a yayin zaman da ta yi.
Idan ba a manta ba, a watan Mayu 2022 ne jami’an ‘yan sanda suka cafke wata mota a Jihar makare da bama-bamai da bindigu.