A ranar Laraba ne ’yan Majalisar Dokokin Jihar Neja suka tsige Shugaban Masu Rinjaye, Honorabul Abba Bala Mohammed da mataimakiyarsa, Binta Mamman, kan zargin sakaci da aikinsu.
Dan majalisa mai wakiltar Bida 1, Bako Kasim Alfa ne ya gabatar da kudirin tsigewar sannan dan majalisa mai wakiltar Wushishi, Mohammed Lokogoma ya goyi bayan hakan.
- Yadda COVID-19 ta yi wa Majalisar Dokokin Neja dirar mikiya
- Shugaba da Magatakardan Majalisar Neja sun kamu da COVID-19
Daga bisani ’yan majalisar sun janye kudirin tsige mataimakiyarsa, Binta Mamman, saboda harbuwa da ta yi da cutar coronavirus a baya-bayan nan.
Amma sun tabbatar da cewa ba gudu ba ja da baya dangane da tsige Shugaban Masu Rinjayen, mai wakiltar Borgu.
’Yan majalisar sun koka game da yadda ya ki halartar zaman nazari kan kasafin kudin Jihar na 2021, duk da cewar ya san muhimmancin halartar zaman.