Majalisar Dokokin Jihar Filato ta zaɓi Nanloong Daniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, bayan da Gabriel Dewan ya yi murabus.
Zaɓen sabon kakakin ya gudana ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar ranar Laraba.
- David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu
- Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana
Zaman ya gudana ne a harabar tsohon gidan gwamnatin jihar.
Hon. Nanloong Daniel, wanda ke wakiltar mazaɓar Mikang wanda kuma tsohon jagoran masu rinjaye ne a majalisar ta tara, ya samu amincewar dukkanin ’yan majalisar 24 don jagorantar su.
Daniel shi ɗan jam’iyyar APC ne.
Zaɓen nasa ya biyo bayan wani zaman sirri da aka yi tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang, tsohon kakakin majalisar Dewan, da sauran ’yan majalisar, domin warware rikicin shugabanci da ke damun majalisar.
Mataimakin akakin ajalisar, Hon. Gwotta Ajang, ne ya jagoranci zaman gaggawar tare da kula da sauyin shugabancin cikin lumana.
Dewan, wanda shi kaɗai ne ɗan jam’iyyar YPP, daga yankin Filato ta Tsakiya, ya ajiye muƙaminsa domin taimakawa wajen kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar.
Murabus ɗinsa na zuwa ne bayan wani dogon lokaci aka kwashe ana rikici bayan korar wasu ’yan majalisar jam’iyyar PDP daga majalisar.