Majalisar Dokokin Delta ta amince wa Gwmnan Ifeanyi Okowa karbo bashin Naira Biliyan hudu domin aiwatar da shirin samar da gidaje ga jama’a.
Wannan ya biyo kudirin da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Chif Ferguson Onwo ya gabatar a zamanta na ranar Talata, inda ya samu goyon bayan Mataimakin Shugaban Majalisar, Christofa.
- INEC ta ayyana ranar zabukan jihohin Bayelsa da Imo da Kogi
- Matasan da suka karkatar da kayan N25m sun shiga hannu
Majalisar ta kuma amince da wata bukatar Gwamnan na karbo wani bashin na Naira biliyan 1.2 daga Bankin Globus domin samar da kudaden aiwatar da shirin bai daya na Hukumar Samar da Ilimin Matakin Farko (UBEC) a jihar.
A wasikar da ya mika wa majalisar, Gwamnan ya ce: “Bisa la’akari da karancin kudaden da jihar mu ke fama da shi yanzu, ya zama dole mu nemo hanyoyin da za mu ci gajiyar shirin samar da ilimin bai daya na matakin farko na kasa.
“Cikin ikon Allah Bankin Globus ya nuna sha’awar samar wa jihar kudaden da ta ke bukata.
“Bayan ba mu takardar tayin da ke nuna sharuddan da suka dace da jihar, bisa la’akari da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
“Za kuma mu biya lamunin ne a shekara guda”, in ji Gwamnan a wasikar da ya aika wa majalisar.