Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kayar da takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben da ya gudana ranar Asabar a Jihar Delta.
Hakan dai na kunshe ne cikin bayanan da Baturen Zaben Jihar, Farfesa Owunari Abraham Georgewill ya gabatar a Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe ta Hukumar INEC da ke Asaba.
A cewar Farfesa Owunari, Obi ya samu kuri’u 341,866 yayin da bai wa Atiku tazara da kuri’u 180,266 wanda ya samu kuri’u 161,600 kacal.
Wannan lamari ya zo a ba-zata kasancewar abokin takarar Atiku, Ifeanyi Okowa, shi ne gwamna mai ci a jihar.
Ga yadda sakamakon zaben ya kaya:
ADC -160
ADP -788
APC -90,183
APGA -3,746
APM -1,028
APP -493
BP -1,016
LP -341,866
NNPP -3,122
MRM -988
PDP -161,600
PRP -334
SDP -3,071
YPP -605
ZLP -3,324
Yawan masu zabe da suka yi rajista: 3,225,046
Masu zaɓen da aka tantance: 667,149
Adadin sahihan kuri’u: 615,341
Kuri’un da aka soke: 39,309
Kuri’un da aka kada: 654,650