Majalisar Dokoki ta Kasa ta umarci ma’aikatanta wadanda ayyukansu ba su zama dole ba da su zauna a gida a ranar Alhamis, takwas ga watan Oktoban 2020.
A ranar ne dai ake tsara shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin badi ga zaurukan majalisun.
- Buhari zai gabatar da kasafin kudin badi a mako mai zuwa
- A kawo wa majalisar kasafin kudi da wuri – Lawan
Umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar ranar Litinin mai dauke da sa hannun sakatarenta, daraktan sashen kula da ma’aikata Mista Felix Orumwense a madadin mai tsawatarwar majalisar.
Kazalika, an aike da kwafin wasikar zuwa manyan jami’an majalisar domin daukar matakin da ya dace.
Wasikar ta ce, “An umarce ni da in sanar da ma’aikatan wannan majalisar cewa a ranar Alhamis, takwas ga watan Oktoba na 2020 cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2021 ga hadakar majalisun Dattawa da na Wakilai da misalin karfe 11 na safe.
“A sakamakon haka, ana shawartar dukkan ma’aikata da su kauracewa ofisoshinsu in banda wadanda ayyuakansu suka zama wajibi.
“Kazalika, umarnin rashin zuwa aikin ya shafi dukkan wasu shaguna, bankuna da sauran cibiyoyin kasuwanci dake kewayen majalisar