Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taron gaggawa don tattauna rikicin da ke faruwa tsakanin Isra’ila da Falasdinawa Zirin Gaza.
Jakadan Majalisar mai kula al’amuran Gabas ta Tsakiya, Tom Wenneslan, ya yi gardin cewa, tsagaita wutar bangarorin biyu suka yi ba mai dorewa ba ne.
- An ga ’yan bindiga da rana tsaka kan babura a cikin garin Katsina
- An kira ni a waya kusan sau 1,000 don tabbatar da labarin mutuwata – Kabiru Nakwango
Ya kuma ce, dole a nemo mafita ta siyaya kafin bangarorin biyu su sake komawa filin daga fadan kuma ya sake kazancewar da mafita a siyasance ya faskara.
Jakadan Rasha Vasisily Nebenzia a taron, ya nuna damuwarsa na tabarbrewar rikicin, wanda ya ce ka iya haifar da babbar matsala ta jinkai da yanzu ake fama a zirin Gaza.
Akalla Falasdinawa 44 wadanda yawancinsu fararen hula ne, da kuma yara 15 ne aka kashe a lokacin da Isra’ila ta soma ruwan bama-bamai a wuraren da kungiyar Islamic Jihad ta ke a yankin Gaza ranar Juma’a.
Daruruwan mutane suka samu raunuka, a cewar hukumar Kula da lafiya ta zirin na Gaza
Kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai na Gaza sun harba dubban rokoki na martani, amma Isra’ila ta ce, ta kakkabosu, wasu kuma ta tarwatsasu a sararin samaniya.
A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra’ila, mutane 3 ne suka jikkata, 31 kuma suka samu kananan raunuka.