Majalisar dinkin Duniya na yin duk abin da ya wajaba don magance tabarbarewar matsalar rashin abinci a yankin Arewa maso.
Mataimakin Kakakin Babban Sakataren Majalisar, Farhan Hak ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar 25 ga Yuli a birnin New York. Yana mayar da jawabi ne a kan wani kashedi da kungiyar Kula da ’Yan gudun Hijira ta kasar Norwey (NRC) ta yi matsalar karancin abinci a yankin Arewa maso Gabas, za ta dada tabarbarewa nan da karshen watan Agusta idan ba a dauki wani mataki ba.
Daraktan NRC a Najeriya, Cheick Ba ya ce, “Rashin zaman lafiya na hana mutane yin noma, kuma yana hana kasuwanci. Wannan yana rage yawan hatsi da kara tsadar kayan abinci, lamarin da ke jawo shiga mummunan hali ga iyalan da yakin ya tarwatsa ciki har da kananan yara dubu 450 da suke fama da rashin abinci mai gina jiki. Samar wa mutane abinci wata mafita ce ta gajeren zango. Amma matsalar za ta kawo karshe ne kawai idan aka magance rikicin kuma jama’a suka dawo garuruwansu suka sake fara sabuwar rayuwa.”
A mayar da jawabin Hak, ya ce an riga an jawo hankalin Majalisar dinkin Duniya a kan halin da ake ciki a Arewa maso Gabas, kuma Najeriya na daya daga cikin kasashe hudu da Majalisar ke nema wa tallafin ayyukan jin kai, hade da Sudan ta Kudu da Yamen da Somaliya.
Hak, ya ce, Majalisar dinkin Duniya ba ta da wani kayyadajjen lokaci da za ta samu kudin da za ta samar da tallafi a Arewa maso Gabas. “Wannan lamari ne da mu da sauran hukumomin majalisar, suke ci gaba da kokari a kai har zuwa lokacin da za a inganta halin da ake ciki,” inji shi.