✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa tana tare da Buhari – Sanata Gaya

Sakamakon matsalar da aka samu lokacin zaben shugabannin Majalisar Dattawa jama’a sun rika zargin cewa majalisar ba ta tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sai…

Sakamakon matsalar da aka samu lokacin zaben shugabannin Majalisar Dattawa jama’a sun rika zargin cewa majalisar ba ta tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sai dai a tattaunawar wakiliyarmu da Sanata Kabiru Gaya, ya ce majalisar tana tare da Buhari:

Aminiya: Ana zargin ’yan Majalisar Dattawa cewa ba su tare da Shugaban kasa Buhari, ko gaskiya ne?
Sanata Gaya: Wato duk yadda aka yi akwai wadansu mutane wadanda suke shuka abin da babu shi. Da farko dai Majalisar Dattawa a shirye take don taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari, idan kuka duba wadanne abubuwa ne Shugaban kasa ya kawo ba a yi ba, kuma idan ana son a yi rigima sai a ce an kawo abu kaza an ki yi.
Babu abin da ya taba kawo wa majalisa muka ce ba mu yi, kwanan nan kwamishina na INEC aka kawo, mutumin Jigawa tsohon Sakataren INEC na da, nan da nan cikin minti goma muka ce tunda Shugaban kasa Buhari ne ya kawo mun amince.
A tafi an kawo mana takardar neman rancen kudi da Jihar Edo ke nema, ni aka ba lura da kwamitin nan, cikin kwana biyu majalisa ta ba ni na je na bincika, kwananmu biyu ba mu yi barci ba, muka zauna muka hada wannan rahoton.
Kamar yadda Buhari ya ce a yi mun amince. Kuma kullum muka tashi, nasararmu ya zamo mun taimaka wa Shugaban kasa ya samu nasara. Yaya za mu taimaka wa Buhari ya yi mulkinsa lafiya ya cika alkawarin da ya yi wa mutanen Najeriya.  Mun san yana cikin matsaloli ga cin hanci da rashawa da ya shafi kasar nan ga kudin kasar nan da aka sace su, yana cikin wani hali da dole mu taimaka wa Shugaban kasa Buhari.  Duk  wanda ke cikin majalisar nan dan Jam’iyyar APC babu wanda bai yarda cewa zaben Muhammadu Buhari Allah ne Ya ba shi, amma da guguwar Buhari, saboda haka muna tare da shi. Zancen ba mu goyon bayansa wadansu ne kawai suke so su yi amfani da wata dama su bata sunayen wasu mutane.
Amma duk dan majalisar da na sani, mu dai da muke APC muna tare da Buhari tare da taimaka wa gwamnatinsa da wasu abubuwa. Kuma ina son mutane su gane cewa in aka dauki Majalisar Dattawa mu 59 na APC 49 na PDP, kun ga ke nan bambancinmu ba yawa, duk da haka duk abin da ya kawo muna tafiya da shi, zancen mutane su kawo wannan rudani na bata suna ko bata majalisa bai taso ba.
Aminiya: Amma wasu na cewa har yanzu Shugaba Buhari bai gana da Shugaban Majalisar Dattawa ba, kuma wannan abu bai yi wa majalisa dadi ba, me za ka ce?
Sanata Gaya: Babu wannan a gabanmu muna yin abin da ya kamata mu yi, kuma muna kokarin mu ga duk wani abu da zai taimaka wa mutane da mulkin Buhari ba mu yi ba. Kun san Jam’iyyar APC, jam’iyya ce da ta hada mutane da yawa daga jam’iyyu daban-daban, wato Jam’iyyar CPC da ACN da ANPP da APGA da wadanda suka bar PDP. To kun ga kowa ya shigo da wani ra’ayin nasa, a hankali za mu narke mu zama daya, mu dunkule mu tafi tare da yardar Ubangiji. Don haka wannan rudani babu damuwa, haka rayuwa take a siyasa.
Aminiya: Wasu sun sa ran cewa majalisa za ta yi koyi da abin da Shugaban kasa da Mataimakinsa suka yi na zabtare albanshinsu da rabi, yanzu ina kunka kwana a kan wannan batu?
Sanata Gaya: Muna nan muna tattaunawa, abin da muka fara shi ne kashi 30 cikin kudin da ake kashe wa a majalisa mun yanke shi. Misali kusan Naira biliyan 30 ke nan muka cire daga cikin biliyan 150.
Kun ga ke nan ba a taba haka ba shekara takwas da nake majalisar. Kuma ba ’yan Majalisar Dattawa kadai ke da kudin nan ba, muna da ma’aikata sun fi mutum dubu shida, kun ga in an dauko ma’aikata takwas suna cikin majalisar, kamar yanzu yadda ma’aikatar shari’a take zaman kanta, mu ma haka muke zaman kanmu.
Ba za a ce kudin da ka ba bangaren shari’a gaba ki daya ka lissafa, alkalai nawa ne, su ma suna da bangare-bangaren a karkashinsu haka mu ma a Majalisar Dattawa, abin da aka turo, ga ma’aikata da suke karkashinmu da yawa, duk wannan da kudin a ke hidimomin.
Abin da muke cewa ga Gwamnatin Tarayya yanzu, idan za ta cire kashi 30 cikin kudin da take kashewa kan sayen wasu na’urori da motoci da biyan wasu abubuwan da ba su da muhimanci, kasafin Najeriya zai dawo kashi 50 kan manyan ayyuka, ba irin gwamnatin baya ba da ake kashe kashi 80 wajen tafiyar da gwamnati, kashi 20 ake manyan ayyuka wa ’yan Najeriya.