✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta yi barazanar ba da umarnin kama Lai Mohammed

Majalisar Dattawa ta yi barazanar bayar da umarnin a kamo mata Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed da sauran shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati bisa kin…

Majalisar Dattawa ta yi barazanar bayar da umarnin a kamo mata Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed da sauran shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati bisa kin amsa gayyatarta.

Tun da farko dai Kwamitin bin Diddigin Ayyukan Gwamnati na Majalisar ne ya gayyace su don amsa gayyatar da Akanta Janar na Kasa ya yi musu.

Kwamitin dai na bincike ne kan Asusun Gwamnatin Tarayya daga shekarar 2008 zuwa 2018.

Shugaban kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide ya shaida wa ‘yan jarida cewa hukumomin da aka gayyata amma suka ki amsa gayyatar su ne Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu, ma’aikatar albarkatun man fetur, Ma’aikatar Lantarki, Ma’aikatar Harkokin Mata, Ma’aikatar Ma’adinai da kuma hukumar kidaya ta kasa.

“Tun kimanin wata guda da ya wuce muka gayyace su don su kare kansu daga tuhumar da rahoton bincike na Ofoshin Akanta Janar na Kasa ya yi musu a 2015.

“Amma da gangan su ka yi kunnen uwar shegu da gayyatar tamu. Wannan karan tsaye ne karara ga doka”, in ji shugaban kwamitin.

Ya ce tarnakin da kin bayyanar tasu ke janyowa na daya daga cikin dalilan da ya sa jama’a da dama ke zargin majalisar da yin tafiyar hawainiya wajen gudanar da ayyukanta.

Ya kara da cewa, “A Najeriya ce kadai mutane za su kashe kudaden gwamnati su kuma yi kunnen uwar shegu in an nemi bayani daga wajensu”.

Sanata Urhoghide ya ce kwamitin nasa ba shi da wani zabi face ya tilasta hukumomin da abin ya shafa da su bayyana a gabansa kamar yadda sashi na 89 na kundin tsarin mulkin kasa yayi tanadi, matukar suka ci gaba da saba gayyatar.