✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta tantance sabbin ministoci 7

Tantancewar na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya sauke wasu ministocinsa bakwai a makon da ya gabata.

Majalisar Dattawa ta tantance mutum bakwai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansu don amincewa da su a matsayin sabbin ministoci.

Majalisar ta shirya tantance Dokta Nentawe Yilwatda, Muhammadu Maigari Dingyadi, Bianca Odinaka Odumegwu-Ojukwu.

Sauran sun haɗa da Hon. Yusuf Abdullahi Ata, Idi Mukhtar Maiha, Dokta Jumoke Oduwole, da Suwaiba Said Ahmad.

Tantancewar ta gudana ne a zauren majalisar bayan ɗage zamanta da ta shirya yi a ranar Talata.

Idan za a tuna a makon da ya gabata ne, Shugaba Tinubu ya sauke ministoci shida, sannan ya sake naɗa wasu bakwai.

Kazalika, ya sauya wa wasu ministoci 10 ma’aikatan da za su ci gaba da aiki.

Majalisar na tantance mutanen ne bisa ƙarƙashin sashe na 147 na Kundin Tsarin Mulki Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).