✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisar Dattawa ta tafi hutun wata daya

Allah Ya bai wa wadanda ke son sake dawowa Majalisar Dattawa nasara a zaben.

Majalisar Dattawan ta jingine zamanta har zuwa wata guda domin bai wa mambobinta damar yin yakin neman zabe yayin da Babban Zaben kasar ya karato.

Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba, yana mai cewa za su dawo zaman a ranar 28 ga watan Fabrairun 2023.

Sanata Ahmad Lawan ya ce majalisar ta dage zamanta daga ranar Laraba domin bai wa ’yan majalisar damar yin yakin neman zabensu domin sake dawowa majalisar ko kuma taimaka wa jam’iyyunsu domin samun nasara.

Ya kara da cewa “Muna addu’ar Allah Ya bai wa wadanda ke son sake dawowa Majalisar Dattawa nasara a zaben da ke tafe.”

Haka kuma Sanata Lawan ya yi kira ga Hukumar Zabe ta Kasa INEC da jami’an tsaro da su tabbatar da cewa an gudanar da sahihi kuma amintaccen zabe a kasar ba tare da samun tashin hankali ba.