Majalisar Dattawa ta sahalewa Gwamnatin Tarayya da jihohi damar ciyo bashin Dala miliyan daya da rabi da kuma Yuro miliyan 995.
Majalisar, karkashin jagorancin Sanata Ahmad Lawan dai ta sanar da amincewar ne yayin zamanta na ranar Laraba.
- Buhari ya sake nada Jelani Aliyu a matsayin shugaban NADDC
- Ba mu tattauna batun Pantami a taron Majalisar Zartarwa ba – Lai Mohammed
Hakan dai ya biyo bayan da Majalisar ta yi nazarin rahoton Kwamitinta Mai Kula da Basussuka na Gida da na Ketare.
Shugaban kwamitin, Sanata Clifford Ordia ne dai ya jagoranci gabatar da rahoton a gaban zauren majalisar.
Basussukan, a cewarsa za a ciyo su ne da nufin kammala manyan ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta kudiri aniyar kammalawa da kuma tallafawa gwamnatocin jihohi.
Za a ranto kudaden ne dai daga cibiyoyin kudi na kasa da kasa, ciki har da Bankin Duniya, Bankin Shige da fice na kasar Brazil da kuma Bankin kasar Jamus.
Sai dai mutane da dama na korafin cewa basukan da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke ciyowa sun yi yawa, ko da yake gwamnatin ta sha kare kanta, inda ta ce tana karbo su ne da nufin ciyar da kasar gaba.