Majalisar Dattawa ta amince da Kudirin Dokar Sake Fasalin Aikin Dan sanda bayan da kwamitin majalisar kan batun ya gabatar da rahotansa a gaban majalisar. Shugaban Kwamitin Kula da Ayyukan ’Yan sanda, Sanata Tijjani Kaura ya bayyana wa majalisar dalla-dallar abin da dokar ta kunsa kafin majalisar ta amince da ita.
Dokar dai za ta canja tsarin zangon mulki na kowane jami’in dan sanda da aka nada a matsayin Sufeto Janar na ’Yan sanda Najeriya zuwa shekara biyar a kan wannan matsayi.
Kudirin dokar ya bayyana kayyadajen lokaci ne na tsawon shekara biyar a maimakon lokacin ritaya da ake amfani da shi.
Kudirin dokar ya nemi Majalisar Dattawa da ita ce kadai za ta tantance Sufeton Janar din ’Yan sanda kamar yadda ita ce take da alhakin tantance Babban Jojin Najeriya da ministoci da kuma jakadun Najeriya zuwa kasashen waje da sauran wasu muhimman mukamai da tsarin mulki ya dora mata.
Dokar ta nemi Hukumar Kula da Harkokin ’Yan sanda ta rika zabo mutum uku daga cikin masu neman mukamin Sufeto Janar domin mikawa ga Shugaban Kasa.
Kudirin ya samar da wata doka da zata rika hukunta duk wani jami’in da aka samu da laifin cin zarafin dan kasa ko kuma kisan kai.
Haka zalika kudirin ya samar da dokar da za ta rika cin tarar masu yin sojan-gona da sunan ’yan sanda kimanin Naira miliyan 5 da kuma daurin shekara biyu.
Haka zalika dokar ba ta canja sunan Hukumar ’Yan sanda ba a cewar dokar tunda sunan yana cikin tsarin mulki na 1999.
Da yake jawabi, Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya yaba wa daukacin ’yan majalisar da suka taimaka wajen samar da kudirin dokar.