✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa za ta yi zaman gaggawa kafin zanga-zangar yunwa

Wannan na zuwa ne bayan da ake ci gaba da shirye-shiryen yin zanga-zanga a faɗin Najeriya.

Majalisar Wakilai za ta yi zaman gaggawa a ranar Laraba game da zanga-zangar yunwa da ake shirin yi a faɗin Najeriya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da aka aike wa ’yan majalisu a ranar 28 ga Yuli, 2024.

Sakataren Majalisar, Dokta Yahaya Danzaria ne, ya sa wa wasiƙar hannu.

Wasiƙar ta ce, “Bisa umarnin Kakakin Majalisa, Abbas Tajudeen, za a yi zaman majalisa a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024.

“Da fatan za ku shirya don halarta, domin za a tattauna muhimman batutuwa. Muna bayar da haƙuri kan katse muku hutu. Mun gode da haɗin kanku.”

Majalisar ta dakatar da zama makon da ya gabata tare da tafiya hutu har zuwa 17 ga watan Satumba.

Ba a bayyana dalilin zaman gaggawar ba, amma ba zai rasa nasaba da zanga-zangar aka shirya yi a ranar 1 ga watan Agusta, 2024, kan matsin tattalin arziƙi.

An samu rarrabuwar kai game da zanga-zangar da aka shirin yi, wanda a gefe guda wasu ke asassa zanga-zangar yayin da wasu ke sukarta.

Amma masu shirya zanga-zangar sun dage kan cew6a za su gudanar da ita kamar yadda aka tsara.

A ranar Litinin, sojoji sun toshe manyan hanyoyin shiga Abuja yayin da zanga-zangar yunwa ta ɓarke a yankin Suleja na Jihar Neja.

An tsauraran matakan tsaro a manyan wurare a Jihar Legas, kamar Ojota, Oshodi, Ojuelegba, da wasu sassan Tsibirin Legas.