✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa za ta binciki Babban Sufeton ’Yan sanda kan zargin Sanata Misau

Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti na musamman don binciken Babban Sufeton ’Yan sanda, Ibrahim Idris, kan zargen-zargen da Sanata Isah Hamma Misau ya yi masa…

Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti na musamman don binciken Babban Sufeton ’Yan sanda, Ibrahim Idris, kan zargen-zargen da Sanata Isah Hamma Misau ya yi masa na cin hanci da rashawa.
Kwamitin wanda ya kunshi Mai Tsawatarwa ’Yan Majalisar, Sanata Francis Alimikhena dan jam’iyyar APC daga jihar Edo a matsayin shugaba, an kafa shi ne bayan da Sanata Misau ya ja hankalin ’yan majalisar  kan batun a lokacin zaman majalisar.
Majalisar ta mika zarge-zargen da Sanata Misau ya yi ga kwamitin da’a na majalisar wanda Sanata Samuel Anyanwu daga jihar Imo yake shugabanta.